ABNA24 : Tun da fari, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Sa’id Khatib Zadeh ne ya sanar da cewa ministan harkokin wajen na Iraqi zai kawo ziyara a yau Asabar.
Bangarorin biyu sun tattauna ne akan hanyoyin bunkasa alaka a tsakanin kasashensu.
Wannan ce ziyarar farko da sabon ministan harkokin wajen na Iraqi ya kawo Iran, tun bayan da ya hau kam mukaminsa.
Baya ga ganawar da zai yi da takwaransa na Iran, zai kuma gana da wasu jami’an gwamnatin kasar ta Iran.
342/